FALALAR KIYAYEWA GA NAFILFILI JERARRU
Daga Ummu Habiba matar Annabi (SAW) tace; Na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su k'ara tabbata a gare shi yana cewa: "Babu wani Bawa musulmi da zai yi Sallah ga Allah a kowace rana raka'a goma sha biyu (12) na nafila bana farillah ba face sai Allah ya gina masa wani gida a Aljannah, ko kuma se an gina masa wani gida a cikin Aljannah, Ummu Habiba tace ban gushe ba ina Sallatan su bayan wannan.
Muslim, cikin littafin Dariqus-Salihin
Wad'annan nafilfili jerarru (Rawaatib)sune, hudu kafin Azzuhar, biyu bayan Azzuhar, biyu bayan Magrib, biyu bayan Isha'i, biyu kuma sune raka'a biyu da ake yi kafin Asuba.
Mu Sani ba wanda zai cika farillai, ya kuma dage da nafilfili face se ya samu soyayya gurin Allah.
Allah ya bamu ikon kiyaye su tare da kyakkyawan niya da Ikhlasi (Amin)