UMMI ZEE-ZEE TAYI ALLAH WADAI GA WANDA SUKAYI MATA KARYA AKAN CEWA TANA NEMAN MIJIN AURE.
A makon da ya gaba tane labarai sukai ta yawo a shafukan sada zumunta akan cewa Ummi Zee-Zee tana neman mijin aure koda talaka ne Indai zai iya daukar nauyin ta a matsayin sa na mijinta to zata aure shi. Biyo bayan wannan labarin ne a jiya tsohuwar Jarumar ta fito a shafin ta na instagram ta mayar da martani akan wannan labarin. Ga dai abinda Zee-Zee take cewa.
Cikin Hotuna Hafsat Idris ta sayi motar miliyan 15
"Salam to Nigerians duk wanda ya rubuta wannan labarin na cewar Ina neman mijin aure to ya cuceni, don yanzu yasa Ko wani Tom and JERRY sai ya dinga aikomin da hotunan sa ta WhatsApp line dina wai zai aure ni, an hanani sakat ba hali in hau online na dinga ganin text messages masu uban yawa wanda ban Isa in iya karanta duka wasikun ba da hotunan maza suma dayawa kala-kala. To Dan girman Allah duk wanda yaimin wannan tsiyar akan cewa Ina neman mijin aure yasan kansa Ko ni bansanshi ba, saboda haka ka dubi darajan Annabi da Alqur'ani kada ka sake yimin karya irin wannan domin maza suna damuna sosai yanzu bayan kuma inada saurayina da nakeso shima yakeso na! Haba mtswwww"
Wannan sune martanin da Ummi Zee-Zee ta mayar akan labarin da aka Yada cewa tana neman mijin aure.