Tambaya:
Assalamu alaikum.
Malam, ina da tambaya kuma zan ji dadi idan za a iya amsa min.
Malam mutum ne balagagge namiji, tun lokacin da ya mallaki hankali kansa ya san cewa yana cikin matsala, amma ya rasa inda zai danganta matsalar, saboda ta daure masa kai, bai taba kawo son mace a zuciyarsa ba ko sau daya, ba ya taba sha’awar mace illa namiji dan'uwan sa. Wannan ba saboda yana kallon batsa ba ne ko kuma yana tare da marasa imanin mutane ba, a’a tun yana karami ake fada masa cewa yakan dauki dankwali ya daura, yanayinsa ma kamar mace yake yi, muryarsa ma idan ba ka san shi sosai ba sai ka dauka mace ce ke magana, abin yana damunsa sosai, ya kai ga idan yayi barci ya yi mafarki da maza yake yi, wato saduwa har maniyyi ya fito masa.
Toh Malam yanzu ya rasa yadda zai sa kansa, wannan wace irin matsala ce? Kuma wace hanya za'a bi wajen samun mafita?
Amsa:
Amen wa’alaikumus salam. To, dan’uwa tabbas ka hadu da babbar musiba, sai dai akwai shawarwari da nasihu kamar haka:
- Ka rinka yawaita istigfari, saboda yana warware matsaloli, sannan sha’awar maza tana kaiwa zuwa ga luwadi, Allah ya hallakar da al’uma gabaki daya saboda suna aikata luwadi.
- Ka dinga yawaita addu’a a lokutan da ake amsar roko, kamar cikin sujjada da karshen dare, saboda Allah zai iya karbar kukanka, ya kare ka daga wannan fitinar.
- Duk lokacin da tunanin namiji ya zo maka a zuciya ka yi kokari wajan kautar da tunanin zuwa wani abu daban mai amfani.
- Shagaltuwa da ayyukan alkairi na taimakawa wajan kaucewa Alfasha.
- Tuna azabar Allah da girmansa, suna taimakawa wajan barin sabo.
- Kada ka dinga kwanciya bacci, sai lokacin da ka tabbatar kana jin bacci, saboda tunane-tunane suna yawan zuwa a wannan lokacin.
- Nisantar abokan banza yana gyara halaye.
- Nisantar cakuduwa da maza zai taimaka maka wajan rashin sanya su a rai.
- Yawaita karatun Alkur’ani na nisanta mutum daga shaidanu, wadanda suke juya dabi’ar mutum.
Tare da cewa akwai mutanen da Allah yake halitta suna da siffofin mata, sai dai ya wajaba ka yi iya bakin kokarinka wajan nisantar kamanceceniya da mata, saboda Annabi S.A.W ya la’anci namijin da yake kamanceceniya da mata, a hadisi mai lamba ta:5546 a Sahihul Bukhari, sifar da ka yi iya bakin kokarinka taki canzuwa, to Allah ba ya dorawa rai sama da abin da za ta iya, kamar yadda aya ta karshe a suratu Bakara take nuni zuwa hakan.
Allah ne mafi sani.