BANBANCI TSAKANIN, MANIYYI, MAZIYYI DA WADIYYI.
Babu jin kunya a cikin sanin addini! Nana A’isha (R.T.A)tana cewa:
“Allah ya jikan MATAN MADINA, Ko kadan KUNYA bai taba hanasu neman sanin addininsu ba”
Dan haka ga banbancin dake tsakanin su kamar haka:
Yadda ake shayin gyada da kanunfari ke warkar da cututtuka
(1a) MANIYYI
Maniyyin namiji: ruwane mai kauri FARI wanda yake fitowa yayin babbar sha’awa kamar saduwa, ko wasa da azzakari. Sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, yayin fitowarsa mutum yakanji matsananci dadi, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino, ko kuma damammen gari, Idan ya Bushe yana kamshin kwai.
(1b) MANIYYIN MACE:
Ruwane TSINKAKKE, MAI FATSI-FATSI, Wani lokacin kuma yana zuwa FARI, wanda yake fitowa yayin babbar sha’awa kamar saduwa, ko yin wasa da farji. Sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, zataji tsananin sha’awa da dadi lokacin daya fito. Kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino ko damammen gari, Idan ya bushe shima yana kamshin kwai. Sannan sha’awarta zata yanke bayan fitowarsa.
Hukuncin fitar MANIYYI shine: yana wajabta wankan tsarki.
Karanta -Wannan hadin na amare ne zalla
(2) MAZIYYI:
Ruwane tsinkakke da yake fitowa, a yayin karamar sha’awa, Kamar tunanin aure ko kuma tuna wacce kakeso, ko matarka, ko kallon matar ko namijin da kike sha’awa.
Haka kuma yana fitowa yayin wasa a tskanin miji da mata, saidai shi baya tafiyarda sha’awa, kuma wani lokacin ba’a sanin yafito. Malamai suna cewa: Maziyyi yafi fitowa mata, fiye da maza.
Hunkuncin sa shine a wanke FARJI gaba daya, da kuma inda ya shafa, sannan kuma a sake al'wala.
(3). WADIYYI
Shi WADIYYI wani ruwane mai KAURI da yake fitowa a karshen fitsari, ko kuma karshen bahaya ga wanda ya jima bai yiba, yana fitowa ga wadanda basuda aure, ko wadanda suka yi nisa da abokin rayuwarsu ta aure, ina nufin namiji ko mace.
Yana daukar Hukunce-Hukuncen fitsari.
Ya Allah kakaramana Imani da fahimtar gaskiya. Allah ka bamu ikon fadar gaskiya komai zafinta ko dadin ta.
Allah shine mafi sani!!!
Dan Allah kudinga yin share dinsa
domin ku sami ladan wadansu su amfana kuma da kukai share kuna da lada