ADDU'OI BAYAN TAHIYYA KAFIN SALLAMA(7)
اللَّهمَّ بعلمِكَ الغيبب وقدرتِكَ على الخلقِ أحيِني ما علمتَ الحياةَ خيرًا لي وتوفَّني إذا علمتَ الوفاةَ خيرًا لي, اللهم إني أسألُكَ خَشيتَكَ في الغيبِ والشَّهادةِ وأسألُكَ كلمةَ الحقِّ في الرِّضا والغضَبِ وأسألُكَ القصدَ في الغِنَى و الفقرِ ، وأسألُكَ نعيمًا لاَ ينفدُ، وأسألُكَ قرَّةَ عينٍ لاَ تنقطعُ, وأسألُكَ الرِّضاءَ بعدَ القضاءِ, وأسألُكَ بَردَ العيشِ بعدَ الموتِ ,وأسألُكَ لذَّةَ النَّظرِ إلى وجْهكَ والشَّوقَ إلى لقائِكَ في غيرِ ضرَّاءَ مضرَّةٍ, ولاَ فتنةٍ مضلَّةٍ, اللَّهمَّ زيِّنَّا بزينةِ الإيمانِ واجعلنا هداةً مُهتدينَ.
Allahumma bi ilmikal ghaibi, wa qudratika alal khalqi, ahyinii maa alimtal hayata khairan liy wa tawaffaniy izaa alimtal wafaata khairan liy, Allahumma inniy as'aluka khashyataka fil ghaibi wasshahadah, wa as'aluka kalimatal haqqi fir-ridaa wal-ghadabi, wa as'alukal qasda fil ghina wal ginaa, wa as'aluka na'eeman laa yanfadu, wa as'aluka qurrata ainin laa tanqadi'u, wa as'aluka arridaa ba'adal qadaa'i, wa as'aluka bardal aishi ba'dal mauti, wa as'aluka lazzatan nazari ilaa wajhika wasshauqa ilaa liqaa'ika fii ghairi darra'a mudirratin, walaa fitnatin mudillah, Allahumma zayyinnaa bi zeenatil imani, waj'alnaa hudaatan muhtadeen.
FASSARA
Ya Allah saboda saninka da abin da yake boye, da kuma IKON Ka a kan hallita, Ka rayar da ni idan Ka san rayuwar tafi alkhairi a gare ni, kuma Ka dauki raina idan Ka san mutuwar tafi alkhairi a gare ni, Ya Allah ina rokon ka jin tsoronka a boye da kuma a sarari, kuma ina rokon ka fadar gaskiya a halin dadin rai da halin fushi, kuma ina rokon ka tsakaituwa a cikin wadata da kuma talauci, kuma ina rokonKa ni’ima da ba ta karewa, kuma ina rokon ka farin cikin da ba ya yankewa, kuma ina rokon ka yarda da kaddara bayan aukuwarta, kuma ina rokon ka rayuwa ta ni’ima bayan mutuwa, kuma ina rokon ka dadin kallon fuskarKa ka da kuma shaukin saduwa da Kai, ba tare da cutar mai cutarwa ba ko fitinar mai batarwa ba, Ya Allah Ka yi mana ado da adon Imani, kuma Ka sanya mu zama masu shiryarwa kuma shiryayyu.