A JIHAR IMO AN KUMA KASHE 'YAN AREWA - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

A JIHAR IMO AN KUMA KASHE 'YAN AREWA



A wasu sababbin hare_hare da aka kai a Jihar Imo an kuma kashe wasu 'yan kasuwa 'yan arewa.

Daily trust ta rawaito cewa an kashe kimanin mutum hudu a yankin Orlu sannan kuma aka kuma kashe wasu a cikin garin Amaka.

Da ake zantawa da wani mazaunin garin Owerri Dr Lawal Yusuf ya dora alhakin kisan akan yan kungiyar IPOB.

Ya Kara da cewa Ko a jiya sai da 'yan kungiyar IPOB suka kaiwa''yan arewa hari suka kashe mutum uku masu sayar da nama. Yau da safe muka binne su.

Duk lokacin da suka hadu da mutanen arewa arewa sai suce sai sun tuhume su waye ya basu izinin zama a yankin Biafra, Ko kuma suce kuna da shiadar zama a yankin?  Idan kace musu a'a sai su kama mutum da dukkan tsiya: Dr Lawal yace an kashe mutanen mu dayawa ta sanadin hakan. 

Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel