HADIN SHAYIN GYADA DA KANUNFARI
Ga wani sirri da nazo muku dashi a yau, kuma wannan sirrin da mace da namiji kowa zai iya amfani dashi domin wannan hadin yana maganin cututtuka da dama Koda mutum yana tunanin babu abinda ke damun sa to kar ya ki yin wannan hadin domin rigakafi ne.
Kuma Kamar yadda nace a baya shi wannan hadin shayin yana maganin cututtuka da dama Kamar su
(1) ciwon basir
(2) sanyi na jiki
(3) thypoid da maleria
(4) hawan jini
(5) ciwon ciki da sauran cutuka da dama
Ga duk wanda keda irin wannan yanayin cutukan to kar yai wasa da wannan shayin na gyada domin idan ana sha za'a Sami waraka. sosai kuma zaiyi wa mutum maganin sauran wasu cutukan da bai ma san yana dasu ba.
YADDA AKE HADA WANNAN SHAYIN NA GYADA
Mutum zai sami gyadar sa mai kyau danya Kamar gongoni 1 idan mai bawo ce sai a bare ta idan kuma a bare aka siyo to shknan sai a wanke ta bayan an bare sai a Sami ruwa Kamar Kofi 1 a daura akan wuta idan ya tafasa sai sai a zuba gyadar a ciki sai a Samu kanunfari Kamar rabin cokali a zuba shi a ciki sai a rufe a barshi ya dafu Kamar na tsawon minti 20 bayan ya dafu sai a tace ruwan domin ruwan kawai ake da bukata sai a sai a bari ya dan huce sai a sha kuma za'a iya zuba zuma Kamar cokali daya ko daya da rabi sai a sha. Amma anaso asha da safe kafin mutum yaci komai za'a iya rabashi 2 asha da safe da yamma Sannan da dare bayan mutum yaci abinci sai a sha.
Zaku iya kallon video domin ganin yadda ake wannan hadin.