WASU ALAMOMI DA AKE GANE BOKA DA SU DA YA KAMATA KU KAURACE MUSU
(1) Ya tambayi sunan marar lafiya da sunan mahaifiyar sa
(2) Ya nemi a kawo masa wani abu na marar lafiya (tufafi, hula, hankici da makamantansu)
(3) Ya nemi a kawo wata dabba da zai yanka, kuma ya fadi siffofinta
(4) Idan ya umarci marar lafiya, ya kauracewa mutane a wani daki da rana bata shiga
(5) Ya nemi marar lafiya kada ya taba ruwa tsawon wani lokaci (sun fi cewa kwana arba'in)
(6) Ya bawa marar lafiya wasu abubuwa da zai binne a kasa
(7) Ya rinka fadar wasu maganganu da ba'a fahimtar su
(8) Daga zuwa ya fadawa marar lafiya sunansa da garinsu da matsalar da ta kawo shi.
(9) Ya bawa marar lafiya wata takarda wadda aka rubuta wadansu haruffa a rarrabe
Tsokaci:
Ku sani Allah baya son shirka! duk wanda yaje gurin boka ya kuma yadda ya yi aiki da maganar sa ya kafirce wa abinda aka saukarwa da Manzon Allah Saw, duk wanda yaje ya ji maganar sa baza'a karbi sallan sa ba ta kwana arba'in.
Idan kinsan/kasan akwai matsala, ki/ki gaugauta tuba zuwa ga Allah..!