WANNAN HADIN NA AMARE NE DA MASU NIYYAR AURE

 

AMARE DA MASU NIYYAR AURE 


wannan wani hadine na musamman wanda ake bukata amare suyi ko masu niyyar aure.


Da farko sai asamu tatacciyar zuma mai kyau a aje gefe daya sai asamu :


  • Dabino (ajuwa).


  • Garin hulba cokali 3.


  • Sai asamu man habbatus sauda dan misra maikyau sai garin ridi cokali 5.


  • Sai gyada itama cokali 5.


Sai a hadesu wuri daya su hadu, sai a rinka sha cokali 3 safe da yamma.


Ko kuma a samu dabino (ajuwa)a hada da nonon rakumi da garin alkama cokali 4 sai a hadasu wuri daya a damasu a rinka sha sau daya arana da daddare.


Kokuma a hada kwa-kwa da dabino maikyau a rinkaci sau daya a rana.


bayan nan sai a hada madara da kankana mai kyau amman kankanar za'a jajjagata sai a hadata da madara a rinka sha safe da yamma.


Wacce ta rasa Budurcinta wato kamar bazawara ko kuma budurwa da aka yiwa fyade(rape) ko kuma Wata hanya daban.


Mata da yawa suna aure cikin fargaba idan suka hadu da (kaddara ta fyade ko kuma saduwa da namiji) kuma hakan yayi sanadin rabuwarsu da budurcinsu don sun san maza da yawa sun fahimci hanyoyin da zasu gane mace idan ta rasa Budurcin ta kuma daga (DAREN FARKO) ango zai iya Fara canjawa amarya soyayyar sa harma wasu suna fadawa zuciyar su bazawara suka auro wato wani ya rigashi kwanciya da ita"_


Idan wannan ta faru dake Zaki iya tsarki da


  • Ruwan dumi


  • Bagaruwa


Na tsawon Wata guda sai kuma matsi. Shi kuma zakiyishi saura sati biyu aurenki


KAYAN HADIN


  • ki daka garin zogale ki tankadeshi.


  • Ki samu man ka danya ( Ana samu a wajen masu maganin gargajiya.


  • Ki samu man zogale ( Ana samu a wajen masu Islamic Medical Centre.


  • Ki samu Karo shine wanda ake tawada dashi kuma ana wanke hula dashi (Ana samun sa wajen masu kayan koli).


  • Ki samu man shanu (ana samun sa a wajen masu siyar rda nono).


Duk ki hada su wajen daya ki kwaba su suyi kamar sa'oi 5 zakiga sun hade sai Kiyi matsi dashi kuma Zaki iya rabashi uku gida 3 wato Kiyi matsi dashi Sau uku a cikin sati biyu.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post