SUNNONI 20 A TSAKANIN MA'AURATA


SUNNONI 20 A TSAKANIN MA'AURATA.

Duk mai buƙatar ya ji dadin aure ya sami farin ciki, to ya yi koyi da Annabi S.A.W akan yadda ya tsara mana yadda zamu zauna da iyali akan sunna ga wasu sunnoni 20 daga koyarwar Annabi saw. :

  • Na  ɗaya  yin  murmushi idan ka  kalli fuskar matarka.

Manzon Allah saw yace murmushinka a fukar Dan uwanka sadaka ne.  Tirmiziy 

  • Na biyu sunbatar mace idan zaka fita (kiss)

Nana Aisha tace MANZON ALLAH saw yana sunbatar matarsa idan zai fita. ABU Dauda 

  • Na uku Amincewa da ita da rashin tuhumar ta, 

Manzon Allah saw ya hana mutum ya dinka fadowa matansa da daddare, idan ya dawo daga tafiya, ka da  ya dinka bin diddiginsu da zargi. Muslum.

  • Na hudu yin sallar dare tare da iyali. 

MANZON Allah saw yace Allah yaji kan mutumin da ya tashi da daddare yana sallah,  kuma ya tashi matarsa,  idan taki ya yayyafa ruwa a fuskarta, saboda yin salloli a cikin gida na nafila tare da iyali yana kara ƙarfin soyyaya da korar sheɗan daga gidan. ABU Dauda. 

  • Na biyar, nuna damuwa da halin da matar mutum take ciki,  na rashin lafiya da bata kuluwa a Wannan lokacin, kamar yadda Annabi saw yake nunuwa iyalinsa. 
  • Na shida ka fada mata kana kaunar ta domin taji dadi,  kamar yadda aka tambayi Annabi saw,  wa yafi so yace Aisha. 
  • Na bakwai Girmama iyayanta da danginta da kawayanta,  kamar yadda Annabi saw yake yiwa kawayan Nana Khadijah bayan rasuwarta. 
  • Na takwas,  yi mata godiya da yabawa akan girki da kwalliya, domin taji dadi.  Wanda baya godewa mutane baya godewa Allah. Hadith 
  • Na tara,  kada ta kawo abinci ko abin sha ya kushe,  kamar yadda Annabi saw, baya kushe abinci,  idan yayi masa ya ci, idan baiyi masa ba ya barshi. Hadith 
  • Na goma. Ya dinka yin hira da tattaunawa da iyalinsa,  da kuma bata damar fadar raayinta.  Kamar yadda Annabi saw yake bawa matansa. Hadith 
  • Na sha daya,  lallashin mace idan ta shiga damuwa,  da kwantar mata da hankali idan ta shiga halin tsoro da firgici. Kamar yadda Annabi saw yake yiwa iyalansa. 
  • Na sha biyu,  kau dakai daga kurakurai da tuno alkhairinta a lokacin sa aka sami matsala. Kamar yadda Annabi saw ya koyar kuma ya nuna a  aikace,   yace :  kada mumini yaki mumina saboda wani halinta da baya so. Domin tana da wani kuma da yake  so. Muslum ya ruwaito 
  • Na sha uku ya dinka kiranta da suna mai dadi kamar yadda Annabi saw,   yake kiran Aisha da Humaira ko kuma Aish ko Ayish. 
  • Na sha hudu,  ya dinka yi mata tsafta da  kwalliya kamar  yadda shima yake so ya ganta. 
  • Na sha biyar,  ya dinka taimaka mata aikin gida,  kamar yadda Annabi saw yake taimaka iyalansa. 
  • Na sha shida, yin wasa da iyali,  kamar yadda Annabi yake yi kuma ya koyawa Jabir cewa idan ya auri budurwa zaiyi mata wasa itama tayi masa,  yayi mata dariya ita ma tayi masa. Bukhari da Muslum suka ruwaito .
  • Na sha bakwai,  yin wanka tare  da Iyali  kamar yadda Annabi saw yake yi. 
  • Na sha takwas,  ya dinka kwanciya yana ta kai da cinyar matar sa , kamar yadda Manzon Allah saw yake yi, tare da Aisha ko tana cikin jinin al'ada. 
  • Na sha Tara,  YA dinka bata abinci a bakinta da cokali ko da hannu,  kamar yadda aka fahinmta daga hadisin Bukhari da Muslum,  cewa ,  Allah zai baka lada har lomar da kake sanyawa a bakin matarka,  wasu malamai sun fassara cewa , ka ciyar da ita kuma ba bata a baki da hannunka,  
  • Na ashirin, Idan matar ka taci abinci ta rage,  ka dauka kaci ragowar,  za taji dadi. Kamar yadda Nana Aisha tace idan naci abinci,  Manzon Allah saw yana ci,  a inda na saka bakina,  haka idan na sha abin sha,  yakan sha ta inda na sha. Muslum ya ruwaito.

Bin tafarkin Manzon Allah shi kadai ne dacewa.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post