SALLAN NAFILA CIKIN DARE (Qiyamul laili)
Annabi s.a.w yace:
.. Mafi falalar Sallah bayan sallan Farillah,itace Sallan cikin Dare).
رواه مسلم
Kuma Manzon Allah (saw) yace:
"Ina maku wasiyya akan ku yi riƙo da sallan cikin dare, domin Dabi'ar mutanen kirki ce ta wadanda suka zo kafin ku, Kuma tana kusantar da ku zuwa ga Ubangijinku, kuma kankarar zunubaice a gare ku, kuma tana goge laifuka, Sannan kuma mai korar cutace daga gangan jiki"
@ صحيح الجامع 4079
Shaykh Ahmad Tijjani Guruntun yace cikin wani karatun sa: Imam Qurdubi yace; "Idan Allah na so ya dake mutum a musulunci ya kafu, babu komawa da baya to Allah se ya yi masa baiwan Qiyamul laili...
Duk abinda ya runguma a musulunci bazai taba komawa da baya ya lalace ba
Shaykh Guruntun, yaci gaba da cewa: Daya daga cikin abinda ke Kafe mutum ya zamo bawan Allah mutumin kirki, abin koyi ga Al'ummah to Qiyamul laili takan zamo dabi arsa
Allah ta'ala ka sanya mu cikin bayinka masu yawan ibadar dare da kyakkyawan niya.