KAYI AURE KADA KAJI TSORON TALAUCI.

 

KAYI AURE KADA KAJI TSORON TALAUCI.

"Sau da yawa samari suna son suyi aure domin su kare kansu daga saɓawa Allah maɗaukakin sarki, to amma kuma sai shaiɗan ya dinga riya musu cewa idan suka yi auren, to lallai nauyi zai hau kansu, kamar na ciyarwa, tufatarwa, da kuma sauran lalurorin yau da kullum, ya manta da cewa shi wanda ya azurtata da waɗancan ni'imomin a gidan iyayenta, shine wanda yake da ikon azurta ta acikin gidan naka ma"

"Wani tabi'i mai suna: Ibrahim An'Nakh'i Allah yayi masa rahama yana cewa: kayi aure, domin lallai wanda yake azurta ta a gidan iyayenta, shine wanda zai azurta ta kuma ya azurta ka acikin gidanka"

تاريخ ابن محرز ١٠٥ 

"Manzon Allah ﷺ, yace: mutane guda uku haqqi ne akan Allah buwayi zai taimake su, me yin jihadi domin daukaka kalmar Allah, da wanda yake son biyan fansa, sannan da kuma wanda yayi aure yana nufin kamewa"

Jam'i at-Tirmiziy: (1655)


*Malam Sanusi Garko*

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post