ILLOLIN MAGGI DUNKULE GA LAFIYAR JIKI


Illar Maggi Ga lafiyar jikin mu!


Zaka ji ana cewa: "Ai gidajenmu na talakawa, sun fi gidajen masu kuďin yan boko, iya miya", kuma fa yawanci ba gaskiya bane, kawai da yake gidajen masu kuďi yan boko, basu jahilci illar dake bayan zaqin Maggi bane, mu ko zaqin Maggi ya hanamu gane illarsa. Maggi dai asalin kamfanin na kasar Switzerland ne, an kirkiri kamfanin a shekarar 1880's, wanda ďan kasuwar nan mai Suna Julius Maggi, ya kirkira.

Na daga cikin illolin Maggi, Su ne: yana sabbaba Neurological problem, da ciwan kai (headache), inflammation ga Koda (liver), akwai kuma hatsarin Metabolic syndrome, da kuma 'Kiba marar ma'ana (obesity), yana kuma sabbaba raguwar appetite, ga kuma illantarwa ga 6angaren haihuwa (reproductive system), da kuma hatsarin kamuwa da cutar daji (cancer).



Duka waďancan illolin da wasu waďanda bamu ambata ba sun samu ne ta dalilin, samuwar Karfen Lead, da kuma sinadarin MSG (Mono-Sodium Glutamate), karancinsu a jiki ba matsala bane, amma yawansu a jiki kan sabbaba ire-iren waďancan cutuka, Kamar shi sinadarin Lead, iya abinda jikinka ke bukata bayan kowani kwanaki 15  shine (0.01ppm) amma a fakitin Maggi akwai (17ppm), haka shima MSG din ba'a so yayi yawa a jikinka, sai ta cutar da kai.

A takaice dai in kana son rabuwa da yiwa sanyi sharri, ta yadda kullum cewa kake sanyi na damunka, a'ah maganin maza, ciwon kai marar Kan gado, toh ka rage cin Maggi, Dan yana mugun illatar da gangan jiki.

Daga

Abdul-Jaleel Muhammad✍️

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post