DA DUMU-DUMI, 'YAN BINDIGA SUNYI AWON GABA DA MA' AIKATAN LAFIYA SU 70 A ZAMFARA


Abin ya faru ne kwanaki kadan bayan 'yan bindigar sun kashe mutane 40 tare da garkuwa da wasu mutane da yawa a wani kauye Sabuwar Tunga dake karamar hukumar Maru. 


Maharan wanda ake zargin 'yan bindiga ne sun kai farmakin ne a kauyen Ruwan Tofa a yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara inda suka yi awon gaba da mutane fiye da 70, har da ma'aikatan kiwon lafiya da kuma yara.


Majiyar mu ta samu rahoton cewa 'yan bindigar sun  kai harin ne a ranar Laraba cikin kauyen akan babura.


Batun tsaro dai a arewancin Nigeria kullum kara ta'azzara yakeyi musamman a yankin arewa maso gabas da yankin arewa maso yamma.

Muna Adduar Allah ya kawo mana karshen wannan tashin hankalin amen.





Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post