https://pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js?client=ca-pub-3044793792529166 src='https://pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js?client='/> YANZU-YANZU | WASU YAN BINDIGA SUN SACE WASU MATA 13 A KATSINA - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

YANZU-YANZU | WASU YAN BINDIGA SUN SACE WASU MATA 13 A KATSINA

 Wasu Æ´an bindiga sun kai hari yankin Æ™aramar hukumar Faskari a jihar Katsina inda suka yi awon gaba da mata suka yi daji da su.

Rundunar Æ´an sandan jihar Katsina ta tabbatar  da faruwan lamarin inda kakakinta Isah Gambo ya ce Æ´an bindigar sun buÉ—e wa motar da matan ke ciki Æ™irar Golf wuta da ke kan hanyarsu zuwa banki a Funtua domin karÉ“ar tallafin da suka samu.

Ya ce mata 13 daga garin Maigora Æ´an bindigar suka yi daji da su amma daga baya uku daga cikinsu sun gudo.

A cewar rundunar Æ´an sandan an kai harin ne ranar Alhamis da safe.

Katsina na cikin jihohin arewa maso yammaci da ke fama da matsalar Æ´an fashi masu garkuwa da mutane domin kudin fansa.

A watan Disamba sama da É—aliban sakandare 300 Æ´an bindiga suka sace kafin daga suka sace su.

Wannan kuma na zuwa a yayin da wasu Æ´an bindigar suka abka makarantar sakandare a Kagara jihar Neja suka saci dalibai a ranar Laraba.

Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel