YADDA AKE NEMAN AURE A MUSULUNCI

 


NEMAN AURE A MUSULUNCI

Musulunci ya tsarawa mabiyansa komai cikin hikimah da kuma kyautatawa, ta yadda babu yadda za'a sami kuskuren hakan a musulunce saidai idan an saka son zuciya aciki"

To kasan yaya ake neman aure ne a musulunci? Idan baka sani ba, to ga wasu hanyoyi wata-ƙila suyi maka amfani ga su Kamar haka;

(1) Namiji idan yaga yarinyar da yake so, dukkanin wasu kyawawan ɗabi'u sun tabbata a kanta, to zai je gidansu yarinyar ne domin neman izinin aurenta a gurin iyayenta, ko waliyyanta.

(2) Idan yaga yarinyar da ya yaba da hankalinta, zai nemi sanin yaya tarbiyyar ta data iyayenta suke, yaya mu'alamarsu da sauran jama'a take a unguwarsu.

(3) Zai nemi sanin halayen ta, shin masu kyau ne ko munana ne.

(4) Zai nemi sanin su wanene ƙawayenta, shin masu tarbiyya ne, ko kuma masu fitsara ne da ziga yarinya tayi burin zaifi ƙarfin wanda zata aura.

(5) Zai yi dubi yaga yanayin danginsu, da iyayenta, ko ƴan-uwanta, shin suna haihuwa ko kuma suna da cutar rashin haihuwa acikin danginsu.


Waɗannan wasu ne daga cikin muhimman abubuwan da za'a duba kenan a ɓangaren ƴa mace kafin a afka izuwa ga aurenta.

Shima namiji ga kaɗan daga cikin abubuwan da za'a duba daga gareshi kafin a yarda a bashi auren yarinya.

(1) Kafin a bashi aure sai an fara duban yanayin roƙonsa ga addininsa na musulunci, da kuma tarbiyyarsa.

(2) Sannan ayi dubi izuwa ga sana'arsa, idan bashida sana'a, to haƙiƙa ba ma'abocin bawa aure bane shi.

(3) Za'a yi dubi izuwa ga danginsa, shin suna da matsalar rashin haihuwa ne ko a'a, ko kuma dai wata rashin lafiyar da ka iya cutar da yarinyar mutane.

(4) Yana kiyaye haƙƙoƙin jama'a, da kuma na ubangijinsa Allah, musamman salloli farillai akan lokutansu.

(5) Shin baya bibiyar ƴan matan banza a waje, ko kuma yana kwashe-kwashe wanda hakan na iya kawo musu matsala acikin rayuwar auren su.

Waɗannan suma kaɗan daga cikin abubuwan da za'a duba daga namiji wanda yake son a bashi auren yarinya.

"Sannan kuma shi neman aure, bawai namiji ne kaɗai yake da haƙƙin furta kalmar neman auren ba, hatta itama macen idan taga namijin da ya burge ta, ta aminta da yanayin riƙonsa ga addini sannan kuma yana da sana'ar yi, to haƙiƙa itama zata iya neman auren nasa, ta hanyar samunsa ta faɗa masa baki da baki, ko kuma ta hanyar yi masa aike da nuna duk wasu alamun da zai fuskanci cewa lallai kina son sa da aure ne"

"Sannan kuma musulunci bai yarda da neman aure akan aure ba, matuƙar masoya biyu suna soyayyarsu sun kai ga batun aure, to lallai haramun ne wani yaje ya shiga tsakanin su yace shima yana son auren wannan yarinyar, ko wata tazo tace itama tana son auren wannan yaron alhalin kuma suna soyayyarsu da juna sun kai ko sun kusa kaiwa batun aure"

Allah kasa mu dace duniya da kuma lahira, Ameen.



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post