SARIN TAZARAR HAIHUWA MARAR AMFANI DA MAGANI
Wannan tsari shi bature ya kira da calendar method ko calendar period wanda akan kauracewa saduwa a wasu ke6antattun kwanaki a yayin da ake neman kaucewa shigar juna biyu saboda wasu dalilai.
Sakon ya kunshi:
■ Abinda ke jawo ciwon ciki ko ciwon mara ga mafi yawan Mata yayin da suke haila da kuma wasu kwanaki can bayan Haila.
■ Yadda ma'aurata zasu yi 'family planning' batare da shan magani ko saka implanon ba.
■ Abinda ke fitowa wasu mata mai kamar majina bayan wasu kwanaki da gama haila
★★★★★
Wannan hanya ta 'family
planning abinda bincike ya tabbatar shine tana da sahihanci na kaso 88 -- 95% cikin dari na hana shigar ciki.
Toh sai dae duk da haka Allah yakan iya canja ikonsa ko da anyi hakan kuma a samu haihuwa, Amma Insha Allah ba'a cika samun ciki ya shiga ba idan aka kiyaye hakan.
A jikin mahaifar mace, (Uterus) idan kuka lura, zaku ga wasu abubuwa kamar hannu guda biyu, daya gefen dama dayan kuma gefen hagun wato bututun da ake cewa (FOLLOPIAN TUBE) a turance wanda ta ciki ararake yake kamar pipe din ruwa... to acan karshe a bakin kowanne follopian in kuka kalli hoton kasa... akwai wani kwanson abu qullutu (Ovary) wanda a cikin sa ne akwai wasu kyayaye.
Duk sanda Mace tayi haila bayan
Jinin ya dauke da kwanaki 14, wancan abu da muka ambata da Qullutu yana sakin wadancan Kyayayen, wadanda sune sinadarin da ake hadawa a samu ďa wato juna biyu'
Wadannan Kyayaye idan aka sake su sukan biyo bututun su shigo cikin mahaifar mace suyi kwanaki 2 wato awanni 48' daga nan idan babu abunda yazo ya ta6asu wato na daga maniyin namiji (sperm) to zasu mutu.
Toh sai dae kafin a saki wadannan kyayayen su tafi mahaifa jiran maniyyin domin samar da ciki, akwai abunda Allah ya halitta a cikin mahaifar mace wanda kan zo ya share mahaifarta sosai (estrogen), domin mahaifar za tayi baqo, wanda bakon kuwa shine wannan Qwan.
Akwai wasu jijiyoyi guda biyu na jini, a gefen dama da hagu na mahaifar mace, idan akazo aka share mahaifar to wadannan jijiyoyin zasu cika da jini sosai, sai su koma ja-ja-wur, suna jiran wannan baqon da zai shigo mahaifa saboda suyi amfani da wannan jinin da suka cika kansu dashi su bawa bakon a matsayin abinci na tsawon awanni 48 da Qwan kan iya rayuwa...
Wanda in qwan ya zarce haka batare da maniyyi yazo ya samesa ba toh lalacewa zai ya mutu...
Shi kuwa Maniyyin namiji yana yin kwanaki 3 wato awanni 72 a cikin mahaifar mace kafin ya mutu, sa6anin na mace dake kwana 24hrs.
Za muci gaba..... .........
Dan wani duk muhinmancin sako idan rubutu yayi yawa bazai iya tsayawa ya Karanta gaba daya ba.
Allah yasa mu gama lafiya!!!