TAƘAITATTUN BAYANAI AKAN NAU'UKA NA SALLAH NAFILA 5
1 0 SALATUT TASBEEH
Daga cikin salloli na nafila masu tarin falala da akeso mutum musulmi yana aikatawa akwai wannan sallah da ake ƙira da salatut tasbeeh, sallah ce da ta kasance cikin nafilolin da suke kankarewa bawa zunubansa wanda yayi da wanda zaiyi.
SIFFARTA
Sahabi Abdullah bin Abbas yake cewa, manzon Allah yacewa Abbas bin Abdilmuɗallib "Ya kai Abbas, Ya kai Baffana shin bazan baka kyauta ko in koya maka wasu abubuwa gudo goma ba wanda idan ka aikata su Allah zai gafarta maka zunubanka, na farkonsu da na ƙarshensu, sabbinsu da tsoffinsu, kuskurensu da gangancin su, ƙananansu da manyansu, na filinsu da na boyensu, shine;
Kayi sallah raka'a hudu, acikin kowace raka'a ka karanta fatiha da surah, bayan ka gama karatun kafin kayi ruku'u sai kace {Subhanallah wal Hamdulillah wa la'ila ha illah wallahu Akbar sau goma sha biyar (15) sannan sai kayi ruku'u, sannan sai ka sake karantawa acikin ruku'un sau goma, bayan ka ɗago daga ruku'u ma sau goma, sannan ka sake karantawa sau goma acikin sujjada, bayan ka ɗago daga sujjada ma sau goma, sannan idan ka sake konawa sujjada kayi sau goma, idan ka dago sau goma, idan ka lissafa shine zai baka sau(75) akowace raka'a, sai ka aikata irin hakan acikin raka'o'in duka. Idan har zaka iya to ka aikata wannan sallah kullum, idan bazaka iyaba to duk ranan juma'a, idan bazaka iyaba to ashekara kayi sau ɗaya, idan bazaka iyaba to kayi sau ɗaya arayuwarka".
أبو داود ١٢٩٨. ابن ماجه ١٣٨٦.
HUKUNCIN TA
Malamai sunyi sabani agameda ingancin wannan hadisin, wasu daga cikin malamai sun raunana shi dan haka awurinsu yin sallar bai halatta ba, saboda raunin hadisin.
Wasu malaman kuma suna ganin halaccin yinta da duk falalan dake cikinta saboda hadisine ingantacce awurinsu, cikin malaman da suka inganta wannan hadisin akwai; *Abubakar Al-Ajuri, Abul Hassan Almaqdisi, Ibnus subki, Imamun Nawawi, Tajus subki, Ibnu Nasiruddeeni Addimashqi, Ibnu Hajar, Imam Assuyudi, Almubarakafuri, Albani, Ahmad Shakir, kuma shine fatawar Abdullah bin Mubarak Allah ya musu rahama gabadaya*
Wannan sallah babu wata surah ƙayyadaddiya da za'a karanta aciki, sannan babu wani lokaci kebantacce na yinta, mutum zaiyine aduk lokacin da yaga dama kuma ya karanta abunda yaga dama.
Sannan Waɗannan zikirori da za'ayi guda goma goman nan za'a yisune bayan gama zikirin ruku'u da sujjada da kuma bayan fadin "Sami'allahu liman hamidah" yayin dagowa daga ruku'u.
Sannan idan mutum yayi rafkanuwa acikin sallar (qabli ko ba'adi ta kamashi) to bazai karanta wancan azkar dinba acikin sujjadar sahwi ɗin kamar yadda Ibnu mabarak ya faɗa alokacin da aka tambayeshi akan hakan.
رسالة التنقيح لما جاء في صلاة التسبيح ١٠٠
Adarasi na gaba zamu tashi akan sallar janaza in sha Allah.