TAƘAITATTUN BAYANAI AKAN NAU'UKAN NA SALLAH NAFILA
0 2 NAFILAR SHIGA DA FITA GIDA
An shar'antawa musulmi yin sallah raka'a biyu alokacin da zai shiga gidansa hakan alokacin da zai shiga anaso yayi sallah raka'a biyu, wannan nafila ba tilas bane sunnah ce, sannan tana zama kariyane ga bawa daga duk wani abu da zai cutar dashi ko iyalansa.
Sahabi Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda yace, Manzon Allah yana cemini "Idan zaka shiga gidanka kayi sallah raka'a biyu zasu hanaka samun mummunan shiga gida, hakanan idan zaka fita kayi sallah raka'a biyu zasu hanaka samun mummunan fita".
صحيح سنن الترمذي ١/١٤٧
0 4 NAFILAR BAYAN ALWALA
An shar'antawa musulmi yin nafila raka'a biyu aduk lokacin da ya sabunta alwala.
FALALAR TA
Hakika falala mai tarin yawa yazo akan duk wanda ya kiyaye wannan nafilar amma da sharadin ya fuskanci Allah da zuciyarsa da fuskarsa acikinsu.
1. Hadisin Uqbatu bin Ammar Allah ya ƙara masa yarda yana cewa watarana nazo na samu manzon Allah yana yiwa mutane magana sai na riske wani abu daga cikin magangunsa ciki yana cewa "Babu wani musulmi da zaiyi alwala ya inganta alwalar sannan ya tashi yayi sallah raka'a biyu yana mai fuskantar Allah da zuciyarsa da fuskarsa face Aljannah ta wajaba agareshi.
صحيح مسلم ٢٣٤
2. Hadisin Uthman bin Affan Allah ya ƙara masa yarda da yasa akawo masa ruwa ya koyawa mutane alwalan manzon Allah, bayan ya gama sai yace musu haka manzon Allah yayi mana bayan ya gama kuma sai yace mana "duk wanda yayi alwala irin wannan alwalar tawa, sannan yayi sallah raka'a biyu batare da yayi taɗi da zuciyarsa ba za'a gafarta masa abunda ya gabatar na zunubansa".
صحيح البخاري ١٥٩
HUKUNCINTA
Wannan nafilar ba wajiba bace sunnah ce, kamar yadda hadisan da muka ambata abaya suka nuna, amma anaso musulmi yana kwatantawa koda kuwa bai dawwama akai ba saboda falalar ta.
0 5 NAFILA TSAKANIN ƘIRAN SALLAH DA SHIGA SALLAH*
Wannan nafila itama tana cikin sallolin nafila da ake kwaɗaitar da musulmi yinsu saboda falalar da take tattare dasu.
HUKUNCIN TA
Wannan sallah ba wajiba bace nustahabbi ce, dalili kuwa shine;
1. Hadisin Abdullah bin Mugaffal yake cewa Manzon Allah yana cewa "Atsakanin kowane ƙiran sallah da Iqama akwai sallah" Manzon Allah sai da ya maimaita sau uku, ana ukun sai yake cewa "ga wanda yaga dama".
صحيح البخاري ٩٣٠
2. Aruwayar Imam Abi Dawud na Hadisin Abdullah bin Mugaffal din manzon Allah yake cewa "Kuyi sallah raka'a biyu kafin tsayar da sallan magriba"
سنن أبي داود ٢٨١
Wannan ruwaya ta Abu dawud tana ƙarfafa mustahabbacin wannan nafila har a sallan magrib wanda wasu mutane ke ganin cewa ita sallan magrib batada lokaci mai tsawo hakan yasa basa bada tazara atsakanin ƙiran sallan da shiga, wanda wannan kuskure ne, yana da kyau abawa mutane daman yin nafila bayan ƙiran sallah. Allah ya mana muwafaqa.
Adarasi na gaba zamu tashi akan Tahiyatul Masjid, Nafilar tuba in sha Allah