TAƘAITATTUN BAYANAI AKAN NAU'UKA NA SALLAH NAFILA 1
Bayan lokaci mai tsawo da muka dauka bamu ɗora akan darussan da mukeyi ba akan sallan nafila da abubuwan da suka shafeta, wanda arubutu na ƙarshe da mukayi munyi bayani akan wasu mas'aloli da suka shafe sallar nafila, wanda a jerengen wannan in sha Allah zamu kawo taƙaitattun bayanai akan wasu daga cikin sallolin nafila, muna rokon Allah ya mana jagoranci.
0 1 SALLAR WALAHA
Sallar walaha sallace ta Nafila da manzon Allah ya sunnantarwa al'ummar sa kuma ya kwaɗaitar dasu akan yinta, kuma tanada falala mai tarin yawa, kaɗan daga ciki shine
1. Hadisin sahabi Abu Zarrin Allah ya ƙara masa yarda yana cewa Manzon Allah yace "kowane mutum yana wayan gari akan kowane gabarsa akwai sadaƙa (ma'ana kowace gaba tana binsa bashi na sadaƙa wajibine sai ya mata), Kowane tasbihi da zaiyi sadaƙa ne, hakanan kowane tahmidi da zaiyi sadaƙa ne, kowane tahlili da zaiyi sadaƙa ne, kowace kabbara da zaiyi itama sadaƙa ce, hakanan umarni da kyakykywa da hani da mummuna shima sadaƙa ne, amma yin raka'a biyu kachal lokacin walaha ya ishi waɗannan duka".
صحيح مسلم ٧٢٠
2. Hadisin Abu Dharda'i Allah ya kara masa yarda yace, Manzon Allah yace Allah yana cewa "ya kai ɗan adam kamun raka'a hudu a farkon yini nikuma zan isar maka ƙarshen sa"
سنن الترمذي ٤٧٥
3. Hadisin Abu Huraira Allah ya kara masa yarda yana cewa Manzon Allah yace "Babu mai kiyaye sallar walaha sai mai tubua zuwaga Allah, sallar walaha sallace ta masu tuba ga Allah".
صحيح ابن خزيمة ٢/٢٢٨
HUKUNCIN SALLAR WALAHA
Hadisan da suka gabata akan falalar wannan sallah ta walaha suna nuni akan sunnah da mustahabbacin wannan sallah din, sai dai babu hujja dake nuni akan wajibancin ta, Malamai sunyi sabani akan shin tilas ne mutum idan ya fara yinta dolene ya dawwama akai ko ba dole ba??
Shaikhul Islam Ibnu Taimiya Allah ya masa rahama yana cewa "Duk wanda ya dawwama akan yin qiyamullaili to ba dole ya dawwama akan yin walaha ba, kamar yadda manzon Allah yakeyi, amma wanda bai dawwama akan qiyamullaili ba to ya dawwama akan walaha, domin walaha badal ne na qiyamullaili".
مجموع الفتاوى. ٢٢/٢٨٤
LOKACIN SALLAN WALAHA
Lokacin sallan walaha yana farawa ne tun daga fitowar rana har zuwa faɗuwar ta, amma lokacin da yafi falala shine lokacin da ranan takeda zafi.
Dalili akan haka shine hadisin Abu Dharda'i da muka ambata abaya, "kamun raka'a hudu a farkon yini..." da kuma hadisin Anas bin Malik Allah ya ƙara masa yarda da manzon Allah yake cewa "duk wanda yayi sallan Asubah acikin jam'i sannan ya zauna yayita ambaton Allah har rana ta fito sannan yayi raka'a guda biyu to yanada ladan aikin hajji da umra cikakku cikakku cikakku"
صحيح سنن الترمذي ١/١٨٢
ADADIN RAKA'O'IN SALLAN WALAHA
An shar'anta mutum ya sallaci sallar walaha raka'a biyu ko hudu ko shida ko takwas koma goma sha biyu, zaiyi su raka'a biyu biyu idan yanaso, idan yaso kuma zaiyi siffofi da muka ambata arubutun baya.
Dalili akan raka'a biyu da hudu shine hadisin Abu zarrin da Hadisin Abu Dharda'i da muka ambata abaya.
Dalili akan raka'a shida kuwa shine Hadisin sahabi Anas bin Malik Allah ya kara masa yarda yace "Manzon Allah ya kasance yanayin sallan walaha raka'a shida"
سنن الترمذي ٢٧٣
Dalili akan raka'a takwas kuwa shine Ummu hani'i Allah ya ƙara mata yarda tace alokacin da akayi fathu makka tazo wurin manzon Allah, sai manzon Allah yayi sallan walaha raka'a takwas.
صحيح البخاري ١١٧٦
Dalili akan raka'a goma sha biyu hadisin Abu Dharda'i Allah ya kara masa yarda yana cewa manzon Allah yace "...duk wanda yayi sallan walaha raka'a goma sha biyu Allah zai gina masa gida a Aljannah..."
صحيح الترغيب والترهيب ١/٢٧٩
Arubutu na gaba zamu tashi akan Nafilar Alwala da ta fita da shiga gida in sha Allah.