TAƘAITATTUN BAYANAI AKAN NAU'UKA NA SALLAH NAFILA

 


TAƘAITATTUN BAYANAI AKAN NAU'UKA NA SALLAH NAFILA

  

NAFILAR SALLAN JUMA'A

   Aƙarƙashin wannan zamu iya raba sallan nafila da akeyiwa sallar juma'a zuwa gida biyu, kafin sallar juma'ar da kuma bayanta, ga bayani akansu duka biyun ataƙaice; 

 NAFILA KAFIN SALLAR JUMA'A

   Babu wata sallah iyakantacciya da tazo daga manzon Allah akan wannan nafilar, manzon Allah ya bartane abude batare da iyakancewa ba,  kamar yadda yazo ahadisin Sahabi Abu Huraira Allah ya kara masa yarda, manzon Allah yana cewa "Duk wanda yayi wanka ranar juma'a ya sanya mafi kyawun suturarsa sannan yasa turare idan yana dashi, sannan ya fita sallan juma'a baije yanata ƙetare wuyan mutane ba, sannan ya sallace abunda zai iya, kuma yayi shiru ya saurari liman har ya idar da sallarsa, to wannan juma'ar zata zame masa kaffara na abunda ke tsakaninta da wacce ta gabaceta". 

 سنن أبي داود ٣٤٣

 NAFILA BAYAN SALLAN JUMA'A

  Hadisi ya inganta daga manzon Allah yana cewa "Idan ɗayanku yayi sallan juma'a to yayi sallah raka'a hudu bayanta". Awata ruwaya kuma yake cewa "Duk wanda zaiyi sallah bayan juma'a to yayi raka'a hudu"

 صحيح مسلم ٨٨١

 Abunda yafi falala kuma yake sunnah ta manzon Allah shine yin wannan sallar agida, kamar yadda hadisin sahabi Ibnu Umar ya nuna, wanda mun ambaceshi abaya.


  NAFILAR DAWOWA DAGA TAFIYA

   Kasancewar tafiya wani yankine na azaba, kuma aduk lokacin da mutum ya fita daga gida da sunan yin tafiya tsammanin rashin dawowarsa shine yafi rinjaye akan dawowarsa, rahama da falala ta ubangiji itace kadai zata bawa mutum ikon dawowa cikin iyalansa yana mai rai da koshin lafiya, abisa wannan dalili shari'a ta shar'anta aduk lokacin da mutum ya tsinci kansa cikin waɗanda sukayi tafiya kuma suka dawo cikin iyalansu lami lafiya da suyi sallah raka'a biyu godiya ga Allah abisa ni'imar dawowa lafiya, dalili akan haka kuwa shine; 

    Hadisin sahabi Ka'ab bin Malik Allah ya ƙara masa yarda yace "Manzon Allah ya kasance idan ya dawo daga tafiya yana fara zuwa masallaci ne yayi sallah raka'a biyu sannan sai ya zauna ya saurari mutane" 

 صحيح البخاري ٤٤١٨

 Wannan sallah ta ƙunshe maza da mata.


  NAFILAR ISTIKHARA 

  Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya karantar da al'ummar sa da cewa duk abunda zasuyi su nemi zabin Allah acikinsa, ya koyar dasu sallar istikhara domin ta maye abunda suka kasance suna aikatawa a jahiliya na chamfi da bokanci.

 YA AKEYIN SALLAN ISTIKHARA 

   Sahabi Jabir bin Abdillah Allah ya ƙara masa yarda yace Manzon Allah ya kasance yana koya mana sallar istikhara  acikin komai namu kamar yadda yake koya mana surah na Alqur'ani, yana cewa "Idan ɗayanku ya nufaci wani al'amari to yayi sallah raka'a biyu ba na farillah ba sannan sai yace { Ya Allah ina neman zabinka bisa ilminka, ina neman qudrarka bisa ikonka, ina roƙonka cikin falalar ka mai girma, domin kai kake qaddarawa ni bana qaddarawa, kai masani ne nikuma bansaniba, kaine masanin abunda ya boyu, ya Allah idan ka san wannan abun alkhairi ne agareni cikin addinina da rayuwata da makomata to ka qaddara mun shi, sannan ka yassaremin shi kuma kamun albarka acikinsa. Idan kuma kasan wannan abun sharrine agareni cikin addinina da rayuwata da makomata to ka kawarmin dashi nima ka kawar dani daga gareshi, sannan ka qaddaramin Alkhairi aduk inda yake kuma ka yardarmin shi}".

صحيح البخاري ١١٦٢

Aƙarƙashin wannan hadisin zamu fahimci abubuwa masu yawa, kaɗan daga ciki sune;

1. Istikhara anayintane acikin kowane irin al'amari, sawa'un babbane ko ƙarami. 

2. Istikhara raka'a biyune na nafila ba na farillah ba.

3. Babu wani lokaci ƙayyadadde nayin wannan sallar, akowace rana kuma kowane lokaci za'a iya yinta.

4. Ba sharaɗine bayan yin istikhara mutum yaji nutsuwa akan wannan al'amarin ba, idan alkhairi ne zai fahimci haka ta hanyar samun saukin abun da kuma ganin albarka acikinsa.

5. Mutum zai iya karanta kowace surah acikin wannan sallar.

6. Malamai sunyi sabani akan wurin yin addu'ar amma zance da yafi inganci shine bayan yin sallama.

7. Istikhara ba'a yinta cikin abunda mutum ke kokonto akansa, anayine cikin abunda mutum ya tsaida ransa ak

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post