MUHIMMANCIN YIN GWAJIN KWAYAR HALITTA KAFIN AURE - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

MUHIMMANCIN YIN GWAJIN KWAYAR HALITTA KAFIN AURE

 


Assalamu alaikum warahamatullah wabarakatuhu! 

Barkanmu da waraka. Yau cikin nufin Allah mun kawo muku wasu daga cikin Binkicen da aka gudanar akan muhimmancin yin gwajin kwayar halitta da ma'aurata ya kamata ace sunyi musamman wanda suke shirin yin aure. 


Baya zama sabon labari, ko wata sabuwar bidi'a, yin gwaje gwaje-gwaje don tabbatar da lafiyar waÉ—anda ke shirin yin aure. Birni da Æ™auye yanzu wannan tsari ya zama gama-gari, ko da yake ba zan ce ko'ina ne tabbas ake hakan ba. Amma lallai jama'a da dama, malamai da Æ™ungiyoyin addini sun Æ™arbi wannan tsari saboda muhimmancin sa, ga tsaron lafiyar ma'aurata da zuriyar da za a samu. 


Muhimmai daga cikin gwaje-gwajen da ake yi su ne na sanin nau'in Æ™wayar halitta wato gwajin Genotype, inda ake Æ™oÆ™arin gane ko Æ™wayoyin halittar jikin ma'auratan ya dace da samun 'ya'ya masu Æ™oshin lafiya. Sai kuma gwajin cutar HIV, wato cuta mai karya garkuwar jiki, wacce daga cikin hanyoyin da ake iya É—auka har da ta hanyar jima'i tsakanin ma'aurata da sauran su. 


Ana Æ™arfafa yin waÉ—annan gwaje-gwaje ne, domin cika Æ™a'idar tabbatar da ingancin lafiyar ma'aurata kafin cika sharuÉ—É—an yin aure, da kuma samar wa yaran da za a haifa ta dalilin wannan aure idan Allah ya yarda, za su rayu cikin ingantacciyar lafiya da kuzari. 


Da dama jama'a sun fi gane wa muhimmancin gwajin cutar HIV, saboda yadda masana kiwon lafiya suke ta Æ™oÆ™arin wayar da kai, a asibitoci, gidajen rediyo da sauran kafofin watsa labarai, domin ganar da jama'a illolin wannan cuta da haÉ—arinta ga lafiyar jikin É—an Adam, ta yadda aka samu wayewa da fahimta, birni da Æ™auye. Matsalar da aka fi samu ita ce a É“angaren gwajin nau'in Æ™wayar halittar jini, wanda ke gadar wa 'ya'yan da za a haifa cutar Sankarar Jini da aka fi sani da Sikila, idan ba a dace da jituwar Æ™wayoyin jinin ba. 


Related Posts:

Binciken masana kiwon lafiya na nuni da cewa, akwai nau'ikan Æ™wayoyin halittar jini kimanin guda biyar zuwa shida da bincike ya tabbatar da su, da suka haÉ—a da AA, AS, SS, CC, AC, da SC. Kowanne É—an Adam za a iya samun sa da É—aya daga cikin waÉ—annan nau'ikan Æ™wayoyin halittar, waÉ—anda daga ciki akwai wasu da haÉ—uwar su take sa a haifi É—a mai lafiya, wasu kuma haÉ—uwar su ta haifar da É—a mai Sankarar Jini, saboda rashin jituwar Æ™wayoyin halittar. Kamar misalin ruwa ne maiÆ™o, ko sinadarin makamashi irin su kanazir ko fetur. Dukkan su dai yanayin ruwa ne da su, amma halittar su daban daban ne! 


Likitoci suna cewa, idan ma'aurata masu nau'ikan halittar jini mai laÆ™abin AA da AA, ko AA da AS, ko kuma AA da AC suka yi aure to, yaran su sun kuÉ“uta daga cutar Sankarar Jini. Amma idan Æ™wayoyin halittar su AS da AS ne, ko AS da SS, ko SS da AC, ko kuma SS da CC ne, ba zai yiwu su yi aure ba sam, don kuwa Æ™wayoyin halittar su ba za su jitu da juna ba, za su iya haifar yara masu Sikila, wato Sankarar Jini, ko da kuwa ba dukkan su. 


Cutar Sankarar Jini kuwa cuta ce mai matukar haÉ—ari ga lafiyar É—an Adam, wacce ke hana yara kuzari ko girma kamar sauran yara, kuma suna rayuwa cikin yawan laulayi da Æ™wambarewar gaÉ“oÉ“in jiki. Kuma akasarinsu ma ba sa tsawon rai. Kawo yanzu dai ba a gano takamaimen maganin wannan mugunyar cuta ba. Sai dai Æ™oÆ™ari da masana sirrin harhaÉ—a magunguna ke yi na gano makarin wannan cuta. Shi ya sa likitoci ke ba da shawarar a daina gaggawar haÉ—a auren masoya mace da namiji da ke sha'awar aure, har sai an tantance nau'in Æ™wayar halittar jinin su ta hanyar yin gwaji. 


Saboda Æ™alubalen da ake fuskanta wajen dakatar da auren da ake gab da É—aura shi bayan a gano rashin jituwar jinin ya kamata a ce tun lokacin da iyaye suka tabbatar da wanda za su bai wa 'yarsu, shi ma kuma namijin iyayen sa suka tambayar masa matar da yake so har suka haÉ—u da iyayen ta aka tattauna tun a matakin farko to, tun kafin a kai ga matakin BADA SADAKI ko ÆŠAURA AURE a je a yi wannan gwajin, saboda babu wasu iyayen da za su ji daÉ—i a ce sai an tara mutane an haÉ—u don É—aurin aure a ce a fasa, saboda sakamakon da gwajin ya bayar. 


Shawara dai ga iyaye a nan ita ce tun kafin tafiya ta yi nisa yaransu su shaÆ™u da juna, har rabuwar su ta iya zama da matsala to, a yi waÉ—annan gwaje gwajen, don sanin makamar alaÆ™ar su. Kada a bari sai abin ya kai wani matsayi da raba su zai zama da wahala, ko kuma ta kai matakin da za su ce tun da ba za su samu damar yin aure ba to, za su je su aikata abin da zai jefa su cikin fushin ubangiji. Ko kuma su masoyan su samu kansu cikin wata matsala da za su jefa rayuwar su cikin tsaka mai wuya! 


Allah ya sa wannan fadakarwa ta amfanar da mu, mu kiyaye kawunan mu da iyalan mu daga faÉ—awa cikin wata rayuwa mawuyaciya.


Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel