MAGANIN MAZINACIN ALJANI[NAMIJIN DARE].
Hanyoyin maganceshi:-
Zamu ambaci guda biyu insha allah za,a dace da amfani da wadannan hanyoyi sune kamar haka:-
HANYA TA FARKO:-
Komawa zuwa ga mahalicci da karatun al-qur'ani:
Da kuma ruko da addu'o'in da manzon tsira ya bamu:
[a] na safiya
[b] da yammaci
[c] dana shiga bayi
[d] da fitowa daga bayi
[e] dana shiga gida
[f] dana fita
[g] da na kwanciya barci
[h] dana tashi
[i] dana sanya sutura
[j] da cirewa
[k] dana cin abinci
duk wadannan manzon tsira ya koya mana su acikin hadisai ingantattu,sai ki duba littafin:-
[HISNUL MUSLIM]
Sannan kuma sai malamai suka bada wasu hanyoyin guda[11] game da macenda take fama da wannan matsalar ko namijin da yake fama da wannan matsalar sune kamar haka:-
[1]Su rinka kiyaye dokokin ubangiji da kuma nisantar laifuffuka na sabo
[2]Yawaita karatun Al-qur'ani ako wani hali mutum ya tsinci kansa kuma ko wani lokaci.
[3]Kyautata sutura [mace]take sanya hijabi daga sama har kasa, hijabin kuma mai kauri, sannan mai fadi ba wanda zai matseta ba.
[4]kiyaye cin halal wanda za,aci ko za,a nema.
[5]Yin sallah akan lokaci tare da kiyaye iliminta ayita kamar yadda manzon tsira ya koyar.
[6]Yawan zama da al-wala da kuma idan za,a kwanta barci kullum.
[7]Yawan karanta.
[Ayatul kursiyyu]
[Amanarrasulu]
[Qul-huwallahu]
[Falaki]
[Nasi]
yayin da za,a kwanta barci.
[8]Yawan karanta Suratul-Bakara acikin gida ko dakin da ake kwana, sannan acire dukkanin wani hoto daga daki.
[9]Yawan karanta [LA'ILAHA ILLALLAHU WAHADAHU LA SHARIKA LAHU,LAHUL MULKU WALAHUL HAMDU,WAHUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIR].sau 100 safe da yamma.