Gwamnoni sun ce za su sake gina kasuwar Sasa dake birnin Ibadan.
Kungiyar gwamnonin Najeriya ta ce za ta ba da gudunmuwa wajen sake gina kasuwar Sasa ta birnin Ibadan da aka kona a rikicin da aka yi tsakanin Yarabawa da Hausawa a karshen makon jiya.
Gwmnan jihar Kebbi wanda ya jagoranci tawagar wasu gwamnonin arewacin Nigeria su hudu zuwa jihar Oyo ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayani a fadar Sarkin Hausawan Sasa Malam Haruna Mai Yasin a birnin na Ibadan.
Gwamna Bagudu ya ce a yanzu haka sun kai wa mutanen da lamarin ya shafa gudunmuwa, sai dai bai yi karin bayani kan gudunmuwar ba.
Gwamnonin na jihohin Arewacin Najeriya sun kai ziyara a jihohin kudu maso yammacin kasar ne a kokarin wanzar da zaman lafiya bayan fadan da ya barke a tsakanin Hausawa da Yarbawa a makon jiya.
Gwamnonin sun hada da na Kano, Abdullahi Umar Ganduje da gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello da gwamnan Kebb Atiku Bagudu.
Akwai kuma Bello Matawalle na Zamfara, wadanda suka ziyarci takwaransu na jihar Oyo Seyi Makinde game da rikicin da ya faru tsakanin Yarbawa da Hausawa a kasuwar Sasa a birnin Ibadan.
Wakilin jarida hausa da ke a birnin na Ibadan ya ce ya kirga kaburbura kusan 12 na mutanen da aka binne daga bangaren Hausawa, yana mai cewa al'uumar Hausawa sun shaida masa cewa mutum 17 aka kashe daga bangarensu.
Rikicin ya kai ga rufe kasuwar tare da kafa dokar hana fita, matakin da ƴan kasuwa Hausawa suka ce ya jefa su cikin mawuyacin hali na rashin abinci da ruwan sha.
Muna Adduar Allah ya kare aukuwar hakan anan gaba amen.
Tags:
Labaran Duniya