DUNIYA INA ZAKI DAMU..
Kamar yadda muke samun labari yanzu, wata baiwar Allah ce ta gudu ta bar Jaririyarta a kwali a daren jiya a wata unguwa da ake kira "Amare" a garin Daura jihar Katsina. Inda ta bar wata wasiyya a cikin rubutu da tayi a takarda a lokacin da ta jefar da jaririryar
Ga abinda ke kunshe a cikin wasikar:
👇
"Ni baiwar Allah nan zan ajiye wannan jaririyar ba tare da zuciyata na so ba, wani bawan Allah ne ya yaudare ni da niyyar zai aure ni, bayan mun shaku sai ya yaudare ni ya mun ciki, shine na haifi wannan jaririyar.
Ina roka mata Allah Ya sa ta fada hannun na nagari, na sanya mata suna Barira".
Wannan shine abinda wannan baiwar Allah ta rubuta a cikin wannan wasikar da ta bari.
Muna rokon Allah Ka shiyar da jama'ar Musulmi, Allah Ka tausaya mana, Kada ka kamamu da laifin da wawayen cikin mu suke aikatawa.