GANDUJE ZAI FARA KAI MASU YIMASA BATANCI KOTU


Gwamnatin jihar Kano da ke Najeriya ta ce za ta gurfanar da duk wanda ya sake shiga gidajen rediyon “yana batanci ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje”.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba Kiru ne ya bayyana hakan.

Ya ce mutane daban-daban suna shiga gidajen rediyo suna yin kalaman batanci ga gwamna na Kano abin da ya ce ba za su ci gaba da yin shiru a kai ba.

Ya kara da cewa: “Muna tattaunawa da Kwamishinan Shari’a domin ganin mun gurfanar da duk wanda ya shiga gidajen rediyo yana bata mai girma Gwamna Ganduje. Mun gaji da irin wannan batanci”.

Sai dai Malam Garba bai bayyana irin kalaman batancin da ya ce ana yi a kan gwamnan na jihar Kano ba.

‘Yan jam’iyyun adawa da masu sharhi kan al'amuran yau da kulluma na kallon matakin a matsayin barazana ga ‘yancin fadar albarkacin baki wanda kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba su.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post