Assalamu alaikum warahamatullah ta'ala wabarakatuhu.
Idan mace tana son mijinta ya ringa jin kamshi alokacin da yake saduwa da ita, sae ta nemi wannan kaya kamar haka:
(1)ANBUR
(2) MISKI
(3)GANYEN MAGAYA
(4) RIHATUL HUBBI
(5) MA’UL MA’I (MA’UL MIYANI)
Wadannan abubuwan da muka lissafa su a sama sune mace zata bukata.
Sai ki hada su wuri daya a cikin kwano ki tafasa su, idan ya huce sai ki nemi butarki mai tsafta ki zuba a ciki, ki dan kara ruwa a ciki. Duk lokacin da zaki kwanta sai kije ki dan kama ruwa dashi duk ki shafe ruwan a gefen farjin ki. Idan kikayi wannan hadin zaki bani labari.
Kuma wannan shi zai hana mijinki ya guje ki, sannan wannan hadin zakiga yanda zaisa ki ringa kamshin farji idan mijin naki ya kusanto ki zai ringa nuna kwadayin sa akan ki, kuma zaki zamo tararuwa agare shi, yayi ta haba-haba da ke. Don haka yan uwa mata ku gwada wannan sirrin yana da amfani matuka .