Dillalan shanu da kayan abinci karkashin shugabancin kungiyarsu ta kasa AUFCDN sun fara yajin aiki daga yau Alhamis a fadin Najeriya bayan cikar wa’adin kwanaki bakwai da suka bai wa gwamnatin tarayya na biya musu bukatunsu.
A ranar Lahadi ne Kungiyar AUFCDN wadda ta hade da Kungiyar Kwadago ta kasa, NLC ta ce, tana son gwamnati ta bai wa mambobinta kariya tare da biyan ta diyyar Naira biliyan 475 saboda kisan da aka yi wa ‘ya’yanta da kuma asarar da ta tafka a lokacin zanga-zangar EndSARS da kuma rikicin kasuwar Shasa da ke garin Ibadan.
Kazalika kungiyar ta bukaci gwamnati da ta bada umarnin janye shingayen binciken ababan hawa da aka kafa a manyan hanyoyin kasar saboda matsalolin da mambobinta ke fuskanta a yayin gudanar da harkokinsu na jigilar abinci da shanu.
Daya daga cikin jiga-jigan kungiyar ta AUFCDN, Hajiya Hauwa Kabir Usman, ta bayyana cewa, an tanadi jami’an kungiyar da za su tabbatar da cewa, ba a yi jigilar shanu da abinci daga arewaci zuwa kudancin Najeriya ba a yayin wannan yajin aikin.