BUHARI YA NADA MATASHI A MATSAYIN SHUGABAN EFFC


Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya nada AbdulRasheed Bawa a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati - EFCC. 


An nada AbdulRasheed Bawa a matsayin sabon shugaban EFCC ne watanni bayan sauke Ibrahim Magu wanda aka zarga da cin hanci da rashawa.

A wasikar da ya aike wa majalisar dattawan kasar, Shugaba Buhari ya ce AbdulRasheed yana da kwarewa a fannin bincike irin na zamba da almundahana da kuma halatta kudin haramun.

 Sanarwar, wadda kakakin shugaban kasa Femi Adesina ya sanyawa hannu, ta ce AbdulRasheed Bawa, mai shekaru 40, yana da digiri a fannin tattalin arziki da kuma digiri na biyu a fannin harkokin diflomasiyya da harkokin kasar waje.

Idan aka tabbatar da nadin nasa, zai kasance mutum mafi karancin shekaru da ya rike mukamin shugabancin EFCC.

A watan Yulin 2020 ne Shugaba Buhari ya sauke Ibrahim Magu daga kan mukamin bisa zarge-zargen cin hancin da ake yi masa - wadanda ke da alaka da yadda ya tafiyar da kudade da kadarorin da aka kwato daga hannun mutane da AbdulRasheed umomi.

Tun bayan sauke shi ne kuma Mohammed Umar yake rikon mukamin shugaban na EFCC wanda kuma yanzu aka nada wani sabon jami'in da zai ci gaba da jagorantar hukumar.

Muna taya Abdulrasheed Bawa murna bisa wannan mukami da akai masa Allah ya taya shi riko amen. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post