AMFANIN ALBASA GA LAFIYAR DAN'ADAM

 

A yau insha Allah mun kawo muku amfanin da albasa take yi a jikin dan adam wanda yana da kyau ace kunsan su domin muhimman cin su. 


Ga kadan daga cikin amfanin ta;

(1) Albasa tana taimakawa ga mutumin da yasuma idan aka fere ta aka sanya masa a kafar hancin sa yana shaka, in sha Allah zai samu tashi in ba ta ajali bace.

(2) Albasa na taimakawa wajen warware ko magance matsaloli irin su farfadiya, ciwon zuciya, ciwon ciki, ciwon suger, asthma, ulcer ta kirji, shock musamman idan aka hada ta da tafarnuwa.

(3) Albasa na taimakawa masu matsalar bugawar zuciya heart attack, idan aka yanka ta danya a saka a cikin abinci aci.

(4) Albasa tana maganin daskerewar Jijiyoyin jini na zuciya.

(5) Albasa tana taimakawa masu ciwon sugar wajen warkarwa musamman a samu babbar albasa ayi kwadon lansir da ita aci kullum.

(6) Albasa tana taimakawa masu hawan jini da masu matsalar zagayawar jini.

(7) Albasa idan aka saka ta cikin Zuma amma sai an yanka ta kullum aci su a haka tana maganin zazzabi, mura, ko ciwon makogwaro, masu ulcer da matsalar urinary tracts infection ma suna iya ci kullum in sha Allah za a samu lafiya.

(8) Albasa na maganin ko taimakawa wajen maganin ciwon Kai na gefe ko daga goshi, idan aka kirba ta ko ita kadai ko da tafarnuwa aka sanya a inda kan yake ciwon.

(9) Wanda Zuma, ko cinnaka, ko kunama ta harbe shi shima za a sama sa wannan a daure da bandage in sha Allah za a samu lafiya.

(10) Albasa tana tsaida habo a rika shakar garin ta ko haka nan a sanya ta a hanci arika shakarta.

(11) Albasa na taimakawa wajen narkar da abinci.

 (12) Albasa na taimakawa wajen warkar da kunar wuta idan aka kirba ta aka dora akan kunar akwai zafi amma za ta bushe ba za ta tashi ba kuma za ta warke cikin kankanin lokaci da yardar Allah.

(13) Albasa tana zama rigakafi ga mata wajen Cancer nono, hanji, da cututtukan mahaifa.

(14) Albasa tana magance matsalar Jijiyoyi.

(15) Albasa na taimakawa wajen magance matsalar amosanin kashi.

(16) Albasa na magance yawan ciwon ciki na yara, musamman yellow din idan aka yanka ta slices(kanana) aka tafasa ta sai a tsame idan ruwan ya huce aba yaro cokali daya karami duk bayan hour daya.

(16) Albasa na taimakawa wajen magance matsalar cunkushewar kirji idan aka kirba ta aka hada ta da man kwakwa aka juye a cikin towel aka daure kirji da shi aka sanya t-shirts da za ta matse kirjin zuwa wani dan lokaci a cire ayi wanka.

(17) Albasa tana taimakawa wajen magance matsalar tari, idan aka samu babbar albasa sai a raba ta biyu a sanya brown sugar akan ko wace sai a bar su zuwa hour daya sai a cinye duka sau biyu za ayi a rana.

(18) Albasa tana taimakawa wajen magance matsalar ciwon kunne, idan aka kirba ta aka samu kamar safa ko tsumma ko towel aka saka a ciki aka daure sai a dora akan kunne din da ke ciwon, ana samun lafiya in sha Allah.

(19) Albasa tana tsayar da jini idan aka samu yankewa kuma za ta zama kamar antiseptic za ta kare fata daga kamuwa da wasu cututtuka a dalilin raunin. Kokuma ayanka albasa daya cikin container a zuba zuma a rufe kamar da daddare zuwa safe a tace sai a rika shan 5ml sau uku a rana idan babba ne.

(20) Albasa tana fitar da guba daga jiki misali ko zazzabi ko mutum yaji jikin sa ya kasa gane masa ko in kana so ma kaji canji a jikin ka to ka jaraba wannan.

(21) A samu albasa daya a yayyanka ta slices amma kanana sai a hada man kwakwa Mai kyau sai a jera a kasan tafin kafa sai a samu farin kyalle ko bandage fari saboda ina son aga irin dattin jiki da za a fitar sai a daure kafar sai asa safa sai a kwanta da safe idan aka tashi sai a cire za a ga abubuwa ayi haka kamar kwana bakwai za aga dattin na raguwa kuma jikin ana kara samun lafiya ko kuma ana kara jin dadin sa. Adaure a jaraba wannan kowa ma yana iya yayi.

(22) Albasa na taimakawa wajen magance matsalar amai, asamu farar albasa ko yellow sai a matseta wato ayi juice din ta sai a zuba cikin tea na na'a na'a cupi daya amma a bari sai tea din ya huce sai asha cokali biyu kanana na tea din na'a na'a bayan minti 5-10 sai asha juice din albasa din Shima cokali biyu kanana sai kuma bayan minti 5-10 asha tea din na'a na'a din haka dai har a daina aman in sha Allah, don yana daukar kamar minti 20 kafin aman ya tafi duka.

(23) Albasa tana tsaftace Gurbataccen iskan da muke shaka, idan aka yanka ta slices sai a ajiye a kusurwar daki ko gida duk wata bacteria ko virus da iskan ya kwaso zata cire ta da yardar Allah.

(24) Albasa tana maganin ko hana cizon kwari idan aka sata a jiki.

(25) Albasa tana hana zubewar gashi idan aka kirba ta aka kara ruwa kadan a rika wanke kai da shi duk sati sau daya.

(26) Albasa tana hana kwari cin shuka ko flowers idan akayi feshin ta.

(27) Albasa tana hana gara cin kaya.

(28) Sanya albasa a jiki na hana fata kuraje.

(29) WHO hukumar lafiya ta duniya ta amince da amfani da albasa wajen jinyar matsalar tari, ciwon  huhu, ciwon kirji, cunkushewar kirji, mura da sauran wasu matsaloli.

Wannan shine kadan daga cikin amfanin albasa da zamu iya kawo muku a wannan lokacin. Allah yasa mu dace amen. 

Kuma duk wanda ya karanta yayi kokari yai share domin jama'a da dama zasu amfana. 

ALHAMDULILLAHI 





Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post